Kungiyar Direbobin Tankar Mai Sun Dakatar Da Jigila Daga Legas Zuwa Arewacin Kasar Nan.
Kungiyar direbobin tanki masu dakon man fetur ta baiwa ‘drebobin umarnin dakatar da jigilar man daga birnin Legas zuwa sassan arewacin kasar daga yau Alhamis har sai abinda hali yayi.
Shugaban kungiyar direbobin tankar na Najeriya Otumba Oladiti ne ya sanarda hakan.
Oladiti yace “tilas ne su yanke hukuncin, saboda matakin da gwamnatin Jihar Neja ta dauka, na haramtawa dukkanin manyan motoci bin hanyoyin da suka ratsa ta cikin garin Minna, babban birnin jihar.
Tun ranar 15 ga watan Satumban nan gwamnatin Neja ta bada umarnin rufewa hanya saboda manyan motocin dakon kayan su ratsa garin na Minna, da zummar soma aikin gyara hanyoyin. Sai dai kungiyar direbobin tankokin man sun ce har zuwa lokacin wallafa wannan labara ba a soma aikin ba.
A cewar kungiyar direbobin tankar, hanyar da yanzu ta rage musu itace wadda ta tashi daga Bidda zuwa Agaie zuwa Lapai sai kuma Lambata, sai dai rashin kyawun hanyar yayi muni matuka, bazasu iya bin wannan hanya ba saboda rashin kyan hanyar na Haifarda hasarar Rayuka da dukiyoyi Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas