Labarai

Kungiyar gwamnonin Arewa sun yi Allah wadai da kisan mutun sama da dari 100 Sakamakon harin ta’addanci a Filato .

Spread the love

Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON ya bayyana a matsayin abin takaici na wannan hare-haren jajibirin Kirsimeti a kan al’ummomin kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na Jihar Filato.

Gwamnan, a madadin Gwamnonin Arewa 19, ya jajantawa iyalai da al’ummomin da abin ya shafa da gwamnati da al’ummar Jihar Filato.

“Abin takaici ne kuma abin Allah wadai ne jin labarin hasarar rayuka sama da 100 da kuma lalata dukiyoyi da aka yi a lokacin wadannan hare-haren, musamman a lokacin da mazauna yankin ke shirin gudanar da bukukuwan kirsimeti.

“Irin wadannan tashe-tashen hankula ba abin tsora ne kawai ba, har ma suna cin karo da ruhin hadin kai da zaman tare da yankinmu ya amince da shi”.

“Dole ne dukkanmu mu ba da fifiko ga zaman lafiya a cikin al’ummominmu. Yanzu fiye da kowane lokaci, dole ne mu sake jaddada aniyarmu ta zaman lafiya da hadin kai ba tare da la’akari da bambance-bambancen da ke tsakaninmu ba.

“Dole ne mu hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, kuma mu tsaya tsayin daka wajen yaki da duk wani nau’in tashin hankali da rarrabuwar kawuna,” in ji shi.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ya yabawa Gwamna Caleb Mutfwang bisa jagorancinsa da kuma yadda ya tafiyar da al’amuran da suka biyo bayan wadannan hare-hare, inda ya tabbatar masa da cewa Gwamnonin Arewa sun tashi tsaye wajen ba shi hadin kai a duk lokacin da ake cikin mawuyacin hali, kuma za su hada kai don samar da zaman lafiya mai dorewa. a jihar Filato.

Ya kuma yabawa jami’an tsaro da ke aiki a yankin, sannan ya roke su da su rubanya kokarinsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin kira ga jama’a da su kara sanya ido cikin gaggawa tare da daukar matakin gaggawa don tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa.

“Ya zama wajibi a gaggauta cafke wadanda ke da hannu a wannan aika-aika domin a hukunta su.”

Gwamnan jihar Gombe ya bukaci al’ummar yankin da su sanya ido tare da gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro duk wani abu da suke da alaka da su domin kawo dauki cikin gaggawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta Bakin Ismaila Uba Misilli
Darakta Janar na Al’amuran Jarida a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe.
Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button