Tsaro
Kungiyar IS Ta Kashe Wasu Kwamandojinta A Tabkin Chadi.
Kungiyar I.S. ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu daga cikin manyan kwamandojinta a tafkin Chadi, kamar yadda wata majiya mai karfi ta tabbatar wa VOA.
Wannan ya biyo bayan mummunar barakar da ta dabaibaye kungiyoyin ‘yan ta’addan ne saboda wasu matsaloli daban-daban.
Masana da dama suna zargin cewa an sami rabuwar kai ne tsakanin ‘yan ƙungiyar sakamokon ra’ayoyi da suka ban-banta.