Addini
Kungiyar Kare Muradin Musulmai Ta Nemi Gwamnan Taraba Ya Daina Nunawa Musulmai wariya
Daga Comr Yaseer Alhassan
Kungiyar kare muradun Musulman Najeriya(MURIC) ta nemi gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba da ya daina nunawa Musulman jihar wariya.
Hakan ya fitone daga shugaban kungiyar, Ishaq Akintola inda yace an hana musulmai da wanda ba kabilar Jukun ba a jihar Taraba amfanar ayyuka da sauran abubuwan more Rayuwa.
Yayi zargin cewa duk shuwagabannin makarantun jihar na jami’o’i Kiristocine sannan kwamishinoni 4 ne kawai Musulmai cikin Kwamishinoni 14 da jihar ke dasu duk da cewa kananan hukumomi 12 daga cikin 16 da ake dasu a jihar musulmai sun fi yawa a cikinsu.
Yace yana kira ga gwamnan da ya daina irin haka, yayi mulkin da zai hada kan jama’ar jiharsa ba tare da nuna banbanci ba.