Kungiyar Kwadago Ta Kasa Reshen Jihar Edo, ta Bijirewa Umarnin NLC ta Kasa.
Shugabannin kungiyar kwadago da mambobin kungiyar farar hula a jihar Edo sun yi watsi da shawarar da shugabannin kungiyar na kasa suka yanke na dakatar da shirin yajin aikin da take shirin yi a duk fadin kasar a Yau Litinin.
Karkashin jagorancin Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) a jihar Edo, Sunny Osayande da takwaransa na kungiyar kwadagon (TUC), Marshall Ohue, da mambobin kungiyar sun mamaye filin wasa na King’s Square Arena a cikin garin Benin babban birnin jihar domin gudanar da zanga-zangar a Yau Dinnan.
A cewar mambobin kungiyar kwadagon da ba su ji dadin shawarar dakatar da shirin yajin aikin da shugabannin kungiyar na kasa suka yi da gaggawa ba tare da tuntubar mambobin majalisar zartarwa ta kasa (NEC) da manyan masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan.
Osayande ya fadawa gidan Talabijin na Channels cewa abin da shugabannin kwadago na kasa suka yi kwanan nan ya raunana yunkurin kwadago a Najeriya, yana mai cewa, “Ba za mu iya ci gaba da kasancewa a hannun wasu Mutane kalilan wadanda za su lamuntar da lamirinmu ba saboda lokaci na gaba idan za mu yi kira ga shugabannin kwadagonmu.
Sun koka kan yadda shugabancin kungiyar kwadago ya raina kokarin da ake yi.
“Ya kamata mu zama muryar talakawa akan titi,” in ji shugaban TUC, Ohue.
Don haka, suka dage kan cewa ya kamata gwamnati ta koma tsohon farashin mai da wutar lantarki ta kuma gyara matatun man kasar nan cikin karamin lokaci.
Kungiyar kwadagon da sanyin safiyar Yau, Litinin ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a yau Litinin bayan ganawa tsakanin shugabannin kwadago da Gwamnatin Tarayya.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar sanarwa da Ministan kwadago da samar da ayyuka, Dakta Chris Ngige ya sanar da hakan.
Shawarwarin dakatar da yajin aikin ya biyo bayan wata yarjejeniya da bangarorin biyu suka cimma da kuma kawar da yajin aikin a duk fadin kasar wanda zai iya dakatar da ayyukan tattalin arziki a kasar.
Kungiyar kwadago, ta jaddada cewa ba a dakatar da yajin aikin ba kuma zata iya dawowa Yajin Aikin Matukar Kwamnati bata Kiyaye Yarjejeniyar suba.
Ahmed T. Adam Bagas