Kungiyoyi

Kungiyar Kwadago Tayi Kira ga Ma’aikata Suyi azumin Kwanaki Uku Kafin Su Tafi Yajin Aiki.

Spread the love

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa Reshen Jahar Neja Comrade. Yakubu Garba Tayi kira ga Duk kan Ma’aikatan Gwamnatin Jahar Dana Kananan Hukumomi da suyi Azumin Kwanaki Uku su Tsaurara Addu’oin Samun Nasara kan Gwamnati.

Garba ya Gargadi Gwamnan Jahar kan Rage Albashin Ma’aikata Na Watan Yuni da Tagabata, Yace “Basu Amince da wannan Tsarin Na Gwamnatin Jahar Ba.

“Yace Sun Baiwa Gwamnati Jahar Daga Nan Zuwa Ranar Juma’a 24- ga wannan watan Idan Gwamnati bata Janye Kudurin taba Zasu Shiga Yajin Aikin Jan kunne Na Kwanaki Uku daga nan Kuma Zasu Tsuduma Yajin Aikin Sai Baba tagani.

Makonni biyu da suka gabatane Gwamnan Jahar Abubakar Sani Bello ya sanar da Cewa ” Za’a Zaftare Albashi Ma’aikatan Jahar Kaso 30 Cikin Dari, Na Kananan Hukumomi Kuma za’a Zaftare kaso 40 Cikin Dari Na Albashin Ma’aikatan Jahar.

Bello yace “An Dauki wannan Matakin ne Saboda Kudin da ake Turowa daga Gwamnatin Tarayya ya Samu Nakasu da Koma baya Dalilin Bullar Covid-19 Inji Shi.

Kungiyar Kwadago da Kungiyar Hada hadar Kasuwanci ta UTC Ne zasu Shiga Yajin Aikin.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button