Kungiyar Lauyoyi Musulmai Ta Goyi Bayan Hukuncin Kisa Kan Wanda Yayi Batanci Ga Annabi Muhammadu S.A.W.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
A sanarwar da shugaban kungiyar reshen jihar Kano Muhammad Sani Garba ya sanyawa hannu.
Kungiyar lauyoyin Musulmai ta nuna gamsuwa da hukuncin kisan da babbar kotun Shari’ar musulumci da ke zamanta a Hausawa dake jihar Kano ta yanke, kan wani Mai suna Sharif Yahya Sharifai, wanda ya amsa laifin yin batanci ga annabi Muhammad SAW.
Kungiyar ta bayyana cewa hukuncin ya yi daidai da dokar Shari’ar musulunci 382(B) kamar yanda wanda ake zargi ya amsa laifin da kansa.
Kungiyar ta shaidawa duniya cewa, musulunci na da dokoki da hukunce-hukunce da duk wanda ya yarda da addinin sai da ya yarda zai yi biyayya ga wadannan dokoki koda sunyi masa dadi ko basu yi masa ba.
Kuma kwansutushin din Najeriya ya bawa kowanne dan kasa damar zabin addinin da ya ke son yi.
kungiyar ta yi Kira ga jagororin addini da su tashi tsaye wajen wa’azantar da mabiyansu da ingantaccen ilimin addinin na musulunci, da zaman lafiya mai dorewa
Bugu da kari kungiyar tayi kira ga Bangaren zartarwa na jahar kano da su bada hadinkai wajen tabbatar da wannan hukunci.
A karshe kungiyar tayi Kira ga al’uma da su zauna lafiya.