Ilimi

Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta koka kan yadda Jami’ar Atiku take diban membobinta.

Spread the love

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta bayyana cewa jami’ar ABTI na kwashe musu membobi inda zuwa yanzu ta dauki malaman jamu’a 25 aiki.

Hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi inda yace saboda rashin biya musu bukatunsu gashi yanzu jamio’i masu zaman kansu na dauke musu membobi.

Yace an san ko wa ke da jami’ar ABTI kuma ta dauki membobinsu 25 aiki, yace jami’o’i masu zaman kansu na morar yajin aikin da ake saboda sai idan babu jami’o’in gwamnati ne zasu samu haskakawa.

Yace gwamnati bai kamata ta kaisu kotu ba dan neman su koma yajin aiki inda yace suma akwai matakan da zasu iya dauka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button