Kungiyoyi

Kungiyar Miyetti Allah Ta Yi Kira Da Ayi Bincike Game Da Mutuwar Makiyaya 68 A Kebbi.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta bukaci Gwamnatin Kebbi da hukumomin tsaro da su binciki zargin kisan gilla da aka yi wa makiyaya 68 a kananan hukumomi hudu na jihar.

Alhaji Othman Ngelzarma , sakataren kungiyar na kasa ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya wallafa a ranar Alhamis.

Ngelzarma ya yi zargin cewa jami’an sakai da a ka fi sani da Dakarkari dake A kananan hukomin Zuru, Sakaba, Fakai da Danko/Wasagu sune wadanda suke zargi da kisan daga 29 ga watan Afrilu zuwa 11 ga watan Ogusta.

A cewarsa guraran da a ka gudanar da kisan sun hada da Zuru, Danko, Maga, Ribah, Joli, Kadurga, Marafa, Kanya, Unashi da kuma Ayyu.

Haka zalika sakataran ya bayyana cewa kungiyar ta matukar damuwa bisa rashin daukan mataki daga hukumomin da suka dace, Injishi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button