Kungiyoyi

Kungiyar ‘Yan Kasuwa magoya bayan Kwankwaso a Jihar Neja Sunyi Kira ga Jam’iyyar PDP Ta Kasa.

Spread the love

A yau Lahadi ne wata kungiyar ‘Yan kasuwa masu goyon Bayan tafiyar Kwankwasiyya a Jihar Neja, tayi kira ga uwar Jam’iyyar PDP ta Kasa da Ta tabbatar ta tsaida, Tsohon gwamnan kano Engr. Rabiu musa Kwankwasko ta Karar Shugaban Kasa a Jam’iyyar ta PDP.

Kungiyar me suna- Kwankwasiyya Youth Marketers Association, tayi kiran ne Ta baking Sakataren ta Comrade. Murtala Ahmad Isah A Ofishin Kungiyar dake A.A Kure Market Minna.

Comrade. Isah a zantawansa da Jaridar Mikiya yace “muna kiran Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa da masu Ruwa da tsaki Na Jam’iyyar da su Tabbatar sun Tsaida Kwankwaso takarar Shugabancin Kasar Nan a wannan Jam’iyyar, domin ceto Kasar daga Matsalar Tsaro da Rugujewar Tattalin Arziki da kasar ke Fuskanta a halin yanzu.

Ya cigaba da cewa “Rashin Iya shugabanci na Gwamnatin APC ne ya kai Kasar nan Irin mummunan Halin da ‘yan Kasar Nan ke Ciki.

Isah yace “Rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa yanzu haka Shi ya haifar da Tsadar Abinci da koma baya ga Harkar Kasuwanci a Arewa da kasa baki daya.

Yace “Ina da Tabbacin Kwankwaso Idan ya zama shugaban kasa a Kasar Nan Zai Kawo Karshen wannan Matsaloli da ‘Yan Kasar ke Fuskanta a Yanzu, Kuma Kwankwaso yanada kwazo Da Jajircewa kan Al’ummar da yake Shugabanta Idan Anyi La’akari da lokacin da yake Gwamna a Jihar Kano Cikin Shekaru 4 kawai na Gwamnatisa Abinda yayiwa Kanawa na alheri Ya Isa ya zama Izina ga ‘Yan Kasar nan Su zabeshi Inji Shi.

Taron Kungiyar Mambobin kungiyar dake Kananan Hukumomi 25 na Jihar Duk Sun Samu Halartar Taron Inji Shi.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button