
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Wata Kungiyar Inyamurai daga Kudancin Najeriya, SESG ta bayyana cewa tunda Najeriya ta dawo tsarin Dimokradiyya, ba’a taba samun shugaban kasar da yawa yankin Inyamurai aiki kamar shugaba Buhari ba.
Kungiyar ta bakin shugabanta Emmanuel Ojukwu ta bayyana cewa ayyukan da shugaban kasar yayi da kuma saka Inyamurai cikin gwamnatinsa a bayyane suke.
Dan haka ya kira ga ‘yan uwansa da su marawa gwamnatin shugaban kasa,Muhammadu Buhari baya.
Ya kuma jabawa hukumar soji inda yace itama a karkashin shugabancin janar Tukur Yusuf Buratai ta yiwa yankin Inyamurai aiki.