Labari Mara dadinji ‘yan ta’adda a jihar katsina sun kashe mutun Tara 9 sun Kuma sace Jama’a da dama..

‘Yan bindiga sun kashe mutane 9, sun sace da yawa a wani sabon hari da aka kai a wasu kauyuka biyun jihar Katsina Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba da ake zargin‘ yan fashin ne sun kai wa wasu garuruwa biyu (2) da ke Batsari a safiyar ranar Asabar Kamar yadda Katsina Post ta ayyana labarin cewa Al’umomin da aka kaiwa harin sune Tsauwa da Gandu.


An ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kashe akalla mutane tara (9), an kuma jikkata wasu da ba a san adadin su ba sannan kuma an yi garkuwa da wasu da dama. Ku tuna cewa ‘yan ta’adda sun mamaye kauyen Tsauwa a watannin da suka gabata a harin ramuwar gayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.