Muna kira ga Gwamnatin jihar Zamfara da Gwamnatin Tarayya da su gaggauta kuɓutar da Ɗalibai Mata sama da 300 da ‘Yan Ta’adda suka sace a Jihar Zamfara – Arewa Media Writters.

Ƙungiyar Marubutan Arewa a kafofin sadarwar Zamani “Arewa Media Writers” ƙarkashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, tana kira ga gwamnatin jihar Zamfara, da gwamnatin Tarayya da su gaggauta kuɓutar da ɗalibai sama da 300 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa dasu a jihar Zamfara.

Idan ba’a manta ba a safiyar Jumma’a da ta gabata wasu ‘yan ta’adda suka sammako makarantar Sakandire ta GGSS Jangebe, dake jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da dalibai Mata sama da Dari Ukku.

Da wannan ne ƙungiyar “Arewa Media Writers” take kira ga gwamnati a kan lallai ya kamata su dage, su kuma zage damtse wajen ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban da suke hannun ‘yan ta’addan.

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana Addu’ar Allah ya ƙara baiwa Iyayen yaran haƙuri, Allah ya kuɓutar da yaran cikin ƙoshin lafiya, Allah ya bamu zaman lafiya mai daurewa. Amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *