Labarai

Kungiyoyi sama dubu dari 150,000 da suka goyi bayan Tinubu sun ce basuyi zaton Tinubu zai juya masu baya ba.

Spread the love

Babban Darakta Janar na kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar APC, Engr Muhammed Kailani, ya ce jam’iyyar ta kasa nuna tsarin bayar da tukuici ga jiga-jigan jam’iyyar ta da suka tsaya mata a lokacin da ta dace.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a Abuja, Kailani ya bayyana rashin jin dadinsa, inda ya bayyana cewa gamayyar kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar APC da ta kunshi kungiyoyi sama da 150,000, gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nuna halin ko-in-kula a kai duk da irin gudunmawar da suke bayarwa a Najeriya da kasashen waje.

Ya ce, “Tabbas jam’iyyar APC a karkashin shugaba Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima tun ranar 29 ga watan Fabrairun 2023, ba ta amince da shugabancin kowace kungiya ta kungiyoyin goyon bayan APC ba dangane da nade-naden mukamai na tarayya. Maimakon haka, ana gabatar da sunayen da ba a sani ba kullun.

“Mambobin mu suna kara rashin hakuri yayin da suke tada tambayoyi na yau da kullun wadanda ba za mu iya amsawa ba. Ba za mu iya ci gaba a cikin wannan yanayin ba. Dole ne Shugaba Bola Tinubu ya dauki mataki domin wadanda suka yi aiki ba tare da gajiyawa ba, suka kashe kudadensu, lokacinsu, da karfinsu wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaben 2023, bai kamata a bar su a hannu wofi ba alhalin wadanda ba a san ko su wanene ba suna cin gajiyar aikin da Basu ne sukayi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button