Kungiyoyi

Kungiyoyin Arewa Sun Bukaci Shugaba Buhari Ya Janye Maganar Karin Kudin Fetur da Lantarki.

Spread the love

A Yau Juma’a ne Wata Kungiyar gamayyar Kungiyoyin Arewa ta nuna Rashin Amincewarta da Karin Farashin Man Fetur da Wutar Lantarki da Gwamnati tayi Ranar Laraba da tagabata.

Sanarwar hakan Na Kunshene a wata takarda da Kakakin Ta Abdul-Azeez Suleiman ya sanyawa Hannu, Inda yace “Bazamu amince da irin salon wannan Shugabancin ba.

Ya kara da cewa “Zamuyi kira ga Sauran Kungiyoyin da Dai dai kun mutane da Kar mu amince da Karin Farashin Man da Lantarki a Irin wannan Yanayin na Tsadar Rayuwa.

Suleiman Yace wannan Gwamnati zuwanta bata zo da sauki ba Sam, yace Ta samu Farashin-

Man Fetur #87 yanzu 151.50

Buhun shinkafa #8500 yanzu #2800

Buhun Masara #3000 yanzu #24000

Takin zamani #2500 yanzu #12000

Farashin Dalar Amurika #195 yanzu #480

Wutar Lantarki ana biyan Kaso 22 ake biya, yanzu kuma kaso 66 za’a biya.

Harajin VAT ana biyan kashi 5 cikin dari, yañzu kuma ana biyan kashi 7.5

Gwamnatin baya ta ciyo bashin $9.6bn. wannan gwamnatin ta ciyo bashin $27bn.

Kuma ga Fatara, Talauci, Yunwa, Fashi da makami, Garkuwa da mutane, Matsalar tsaro, Cin Hanci da Rashawa, Rashin Aikin Yi, Fyade, Da Sauran Fitin Tunu da suka Addabemu Saka makon Rashin Iya Shugabanci Ya mamaye wannan Gwamnatin.

Ko a Jihar Ogun ma wasu Matasa Sun yi zanga zangar Kin Amincewa da Karin Farashin Fetur da Lantarki da Gwamnatin Tarayya tayi.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button