Rahotanni

Kunji Rabo: Sulaiman Isah Matashi Dan Jihar Kano Wanda Ya Auri Baturiya ‘Yar Amerika Ya Zama Sojojan Amurka

Spread the love

Wani dan Kano mai suna Suleiman Isah da ya auri wata Ba’amurke mai shekaru 46, Janine Sanchez, ya shiga cikin rundunar sojan kasa ta California, da ke ajiyar sojojin Amurka.

Dangane da bayanan, Rundunar Sojan Kasa ta California ta ƙunshi sojoji 18,450.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Isah ya saka hoton sa sanye da kakin sojojin Amurka tare da sanya wa taken “Alhamdullillah- na godewa Allah”.

Masoyan biyu, wadanda suka hadu a shafukan sada zumunta, sun yi aure ne a ranar 13 ga Disamba, 2020.

Ms Janine, wata mai dafa abinci ce da ke birnin Lindon na jihar California, ta je Najeriya domin bikin auren.

Daurin auren wanda ya gudana a Masallacin Juma’a na MOPOL Barracks 52 da ke Panshekara a karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, ya samu halartar dubban jama’a daga ciki da wajen jihar.

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, wanda kuma dan uwa ne ga mahaifin angon, ya tsaya a matsayin wakilin Janine (waliy).

Da yake tsokaci kan sabon lamarin a shafinsa na Facebook, Sani ya taya jami’in murna tare da caccakar wadanda suka yi masa caccaka a lokacin da yake goyon bayan hadakar.

“Sun soki ni kan wannan auren na kabilanci kuma yanzu Suleiman Isah ya yi aure cikin farin ciki kuma ya shiga cikin rundunar sojan kasa ta California. Ina taya ku murna,” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button