Duniya ina zaki damu? : Wasu da ba’a san ko suwaye ba sun cinnawa wata maƙabarta wuta.


A yayin da mamaci yake kwance a kushewa kamata yayi ace ya huta, ya samu salama ta rayuwa bayan mutuwa, to amma aiyukan mutane, masu illata muhalli da abinda ke cikin muhallin, yana nema ya zama kadangaren bakin tulu wajen tabbatar da wanzuwar jindadin matattu a kushewarsu.

Hakane ya faru yayin da mutane mazauna unguwar dake Maikalwa, a can ƙaramar hukumar Kumbotso dake jihar Kano suka tashi da wani abu mai ban al’ajabi da kuma ban haushi a ƙarshen makon nan daya gabata.

Wasu da ba’a san ko su wanene ba, suka cinnawa maƙabarta wuta, inda suka mata ƙurmus kamar an aiko su.

Mutane da yawa sunyo agaji domin kashe wutar, amma dakyar aka samu aka shawo kanta.
Kamar yadda Malam Sani wanda yake maƙocin maƙabartar ya bayyana , cewa yayi :

“Ansha wahala kwarai da gaske domin ganin an shawo kan gobarar, wanda mata da yara na daga cikin waɗanda sukayi ta kokarin kashe gobarar duk da wahalar da suke sha na azumi”.

Majiyar Mikiya tayi tabbatar da cewa kabarurruka masu yawa ne suka ƙone ƙurmus.
To Allah ya kyautata makwanci, ya kyautata namu zuwan, su kuma masu sakawa maƙabarta wuta, Allah ya shirye su.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *