Shin ka san wani kuɗin Najeriya bayan Naira?

Shin Ka San Wani Kuɗin Najeriya Bayan Naira?

Kuɗin Najeriya kenan a loƙacin yana matsayin Pound 💷 a Shekarar 1967

Saidai kuma Chief Obafemi Awolowo a loƙacin yana matsayin Federal Commissioner of Finance na Najeriya shi ne wanda ya chanja kudin ƙasar daga Pound zuwa ₦Naira da Kobo a ranar 1 Janairu 1973.

An ƙirƙiri sunan kalmar ‘Naira’ daga ‘Nigeria’ sannan sunan ‘Kobo’ daga ‘Copper'( wato jan ƙarfe) saboda da jan karfe aka yi kuɗaɗen

A loƙacin ana chanjin kuɗin Najeriya duk ₦naira 2 tana daidai £1 na Burtaniyya naira 1 kuma tana dai-dai da $0.6 na Amurka

Amma kuɗaɗen naira da ake amfani dasu a yanzu ₦5 ita ce wacce aka fi daɗewa ana amfani da ita tun daga ranar 2 July 1979 har izuwa yau , Saidaai a ranar 30 September 2009 aka chanjawa kuɗin fasali daga takarda zuwa leda

A gaban kuɗin naira 5 akwai hoton farkon Firayiministan Najeriya wato Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa wanda aka haifeshi a shekarar 1912 sannan ya mutu a shekarar 1966

A bayan kuma naira 5 akwai hotunan ƴan rawar Nkpokiti daga kudancin Najeriya.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *