• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
JaridarMikiya
Advertisement
  • Home
    • Home – Layout 1
    • Home – Layout 2
    • Home – Layout 3
    • Home – Layout 4
    • Home – Layout 5
    • Home – Layout 6
  • Tech

    These Are the 5 Big Tech Stories to Watch in 2017

    With 150 million daily active users, Instagram Stories is launching ads

    Trending Tags

    • Nintendo Switch
    • CES 2017
    • Playstation 4 Pro
    • Mark Zuckerberg
No Result
View All Result

Home Kunne Ya Girmi Kaka

TARIHIN TSOHON BIRNIN HAUSAWA; KAFIN DABGA…

Sabiu1 by Sabiu1
May 15, 2020
in Kunne Ya Girmi Kaka
0
0
SHARES
1
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, GGA..

Daga cikin tsoffin biranen da Maguzawa suka kafa waɗanda kuma suka shahara a ƙasar Kano tun kafin zuwan jihadin Fulani akwai wannan tsohon garin mai suna ‘Kafin Dabga’.
Wani mashahurin mayaƙi bamaguje mai Suna ‘Dabga’ ne ya sari garin, shine kuma yayi masa kafi gagarumi domin kuɓuta daga dukkan harin mayaƙan wancan zamani, don haka ake kiran garin da suna Kafin Dabga.

Garin ya haɓaka, ya shahara, kuma ya samu ɗaukaka. A baya ance zagaye yake da ganuwa, wadda aka yiwa ƙofofi guda huɗu. A kowacce kofa mace da namiji ne suka tsaya aka yaɓe su da ransu saboda surkulle, sannan da wata ƙaya sarƙaƙiya ake rufe kofar shiga birnin ba da ƙofa ba. Don hakangarin ya kasanxe mai tsananin uytsaro.

Idan yaƙi yazo, daka ake sanyawa ayi da dare, sai mayaƙa su shirya da hanzari. Masu kwari da baka su hau saman ganuwa, masu masu da takubba su shige surƙuƙi suna sauraron ko-ta-kwana.

Daga cikin sarakunan da ake iya tuna sunayen su a wannan gari, ance sunan Sarkin Kafin Dabga na farko Dugaji, Bamaguje ne, yayi wannan sarauta kimanin shekaru 400 da suka gabata, ko da yake tsufan kukokin garin da marinar garin na iya kaiwa sama da waɗannan shekarun.

Amma dai kwatancin shekarun da ake tsammanin an soma sarauta a garin kenan.
Bayan mutuwar sa sai shi Dabga yayi mulki, wanda asali ance ya zamo tamkar uba ne mai ɗora wanda yake so shugabanci a garin.
Daga shi sai Also, sannan sai Abdullahi ya fara mulki a zamanin da Fulani suka karɓe sarauta.

Akwai manyan gidajen da har yanzu ake ambata a garin, waɗanda sukayi gadon shugabancin garin, da kuma jarumta tun kafin jihadin fulani, misalin su shine; Gidan Nazundumi, Gidan Dankali, Gidan Butsatsa, da Gidan Gigo.

KUKAR ƳAR FULANI
Akwai wata kuka mai tarihi a wannan gari mai suna kukar ƴarfulani. Ita ƴar fulanin aljanna ce wadda ake da yaƙinin akan wannan kuka gidan ta yake.

Ance a zamanin baya, tana taimakon garin lokacin da yaƙi ya taso, ko kuma wani mugun abu ya nufo garin, inda take sanya sarƙa ta kanan-naɗe mahara.
Ance kuma a zamanin mulkin sarki Abdullahi na garin, yana sanyawa a kai mata ƙwaryar nono da farin goro duk ranar juma’a, ita kuma takan yin shewa da godiya yadda duk wanda ke garin sai ya ji.

TARWATSEWAR KAFIN DABGA..
Kafin garin kafin Dabga ya samu raguwar mazauna, ya kasance shahararre mai cike da mutane wanda ya kasance daga gari-gari akan zo masa don yin fatauci.

Sannan garin yayi yaƙe-yaƙe da biranen dake kusanci da ma na nesa misalin Gammo da Ƙiru, har ma ana cewa ba a taɓa cin garin da yaƙi ba.

Sai dai wata annoba da ta faɗawa garin ce tayi sanadiyyar ɗaiɗaicewar sa.

Ance wata baƙar aljana ce ta rinƙa halaka mutane.

Idan dare yayi sai tayi shewa, tace ‘Kun Taru?’, to fa duk wanda yayi ko da gyaran murya a wannan daren ba zai wayi gari ba. Daga nan aka sanyawa annobar suna ‘Kun-Taru’.

Don haka aka rinƙa wayar gari da gawarwakin mutane burjik waɗanda ta halaka, hakan yasa mutanen garin da dama suka ƙaurace masa.

A yanzu dai, garin Kafin Dabga yana nan ƙarƙashin garin Karaye, a jihar kano.

Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta Amince da kafa kwalejojin ilimi

Next Post

Atiku Ya Shawarci Buhari A Twitter

Sabiu1

Sabiu1

Next Post

Atiku Ya Shawarci Buhari A Twitter

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Stay Connected test

  • 23.6k Followers
  • 99 Subscribers
  • Trending
  • Comments
  • Latest
Da ‘dumi’dumi: Gwamna El Rufa’i da wasu Gwamnoni na shirin ballewa ga tafiyar Bola Tinubu.

Da ‘dumi’dumi: Gwamna El Rufa’i da wasu Gwamnoni na shirin ballewa ga tafiyar Bola Tinubu.

July 19, 2022
Da ‘dumi’dumi: Babbar kotun tarayya ta bayarda Umarnin a mikawa Sanata Ahmad lawan sammaci ta ko wacce hanya domin zuwa kotu.

Da ‘dumi’dumi: Babbar kotun tarayya ta bayarda Umarnin a mikawa Sanata Ahmad lawan sammaci ta ko wacce hanya domin zuwa kotu.

July 14, 2022
Da ‘dumi’dumi Dan majalisar tarayya da na jiha tare da tsohon Minista sun fice daga Jam’iyar PDP sun koma jam’iyar NNPP ta kwankwaso Mai kayan marmari.

Da ‘dumi’dumi Dan majalisar tarayya da na jiha tare da tsohon Minista sun fice daga Jam’iyar PDP sun koma jam’iyar NNPP ta kwankwaso Mai kayan marmari.

July 15, 2022
Tonon Silili: Yadda muka shigo da ‘yan ta’addan Fulani daga Mali, Saliyo, Senegal da sauransu domin su taimaka mana a zaben 2015 – Jigon APC Kawu Baraje

Tonon Silili: Yadda muka shigo da ‘yan ta’addan Fulani daga Mali, Saliyo, Senegal da sauransu domin su taimaka mana a zaben 2015 – Jigon APC Kawu Baraje

August 3, 2022

Ina son aure yaro matashi dan shekara 25 zuwa 30~ Inji shugabar kungiyar muryar Zawarawa ta Kano

14

CBN ya rabawa Matasa mutum sama da dubu bakwai naira Biliyan biyu da digo hudu (2.04b) a karkashin tsarin NYIF.

6

Kasuwancin Cryptocurrency Haramun ne zalla ~inji Sheikh Bin Usman.

4

Duk Wanda Ya Cika Neman Bashin Ranche Karkashin Tsarin NYIF Ya Gaggauta Shiga Dashboard, Ya Sabunta Asusun Ajiyarshi Na Banki

3
Badakala: Takardu sun nuna Bashir Ahmad ya ci gaba da karbar albashi ba bisa ka’ida ba watanni bayan ya yi murabus daga mukamin mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai.

Badakala: Takardu sun nuna Bashir Ahmad ya ci gaba da karbar albashi ba bisa ka’ida ba watanni bayan ya yi murabus daga mukamin mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai.

August 16, 2022
Buhari na iya cigaba da ciyo bashi daga yanzu har abada, Amurka da Biritaniya su ma sun ci bashin kudi – Shugaban APC Adamu

Buhari na iya cigaba da ciyo bashi daga yanzu har abada, Amurka da Biritaniya su ma sun ci bashin kudi – Shugaban APC Adamu

August 16, 2022
Buhari yana kokari, mulkinsa cike yake da rashawar jami’ai, amma haka yake yaki dasu – Keyamo

Buhari yana kokari, mulkinsa cike yake da rashawar jami’ai, amma haka yake yaki dasu – Keyamo

August 16, 2022
Sanata Uba sani ya karyata batun cewa ya Kai Kudri gaban majalisar domin kirkiro Jihar zazzau.

Sanata Uba sani ya karyata batun cewa ya Kai Kudri gaban majalisar domin kirkiro Jihar zazzau.

August 15, 2022

Recent News

We bring you the best Premium WordPress Themes that perfect for news, magazine, personal blog, etc. Check our landing page for details.

Follow Us

Browse by Category

  • Addini
  • Al'adu
  • Alqur'ani Tafarkin Tsira
  • Fina finai
  • Ilimi
  • Kasashen Ketare
  • Kasuwanci
  • Kimiya Da Fasaha
  • Kungiyoyi
  • Kunne Ya Girmi Kaka
  • Labarai
  • Lafiya
  • Mata
  • Nishadi
  • Rahotanni
  • Sana'o'i
  • Sanannu
  • Siyasa
  • Sports
  • Startup
  • Tech
  • Travel
  • Tsaro
  • Tsegumi
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • World
  • Zamani
  • Zamantakewa

Recent News

Badakala: Takardu sun nuna Bashir Ahmad ya ci gaba da karbar albashi ba bisa ka’ida ba watanni bayan ya yi murabus daga mukamin mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai.

Badakala: Takardu sun nuna Bashir Ahmad ya ci gaba da karbar albashi ba bisa ka’ida ba watanni bayan ya yi murabus daga mukamin mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai.

August 16, 2022
Buhari na iya cigaba da ciyo bashi daga yanzu har abada, Amurka da Biritaniya su ma sun ci bashin kudi – Shugaban APC Adamu

Buhari na iya cigaba da ciyo bashi daga yanzu har abada, Amurka da Biritaniya su ma sun ci bashin kudi – Shugaban APC Adamu

August 16, 2022
  • About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact

© 2022 JaridarMikiya - Design by NGWebDev.

No Result
View All Result

© 2022 JaridarMikiya - Design by NGWebDev.