Zamfara ta kashe nera biliyan biyu wurin bada tallafin Ramadan 

Gwamnatin jihar Jigawa tace ta kashe nera biliyan biyu wurin siyan kayyayi domin rabawa mutane a rukuni kala kala a matsayin tallafin Ramadan.

Wannan bayanin yazo ne daga kwamishinan labarai na jihar Ibrahim Dosara a wata sanarwa da akayi ranar lahadi.

Yace chiaman din kwamitin rabon tallafin Ramadan na wannan shekarar wanda kuma dan speaker ne na yan majalissu, Nasiru Margaya, ya tabbatar da cewa wannan tallafin zai isa ga wadan da suka dace a garin.

Yace sipika din ya riga ya hada kwamiti wanda zasu taimaka wurin yin wannan rarrabo.

Dosara ya kuma karawa da cewa an cika motocin daukan kaya har guda dari hudu da hamsin wadan da suka kunshi buhunnan shinkafa, wake, gero, masara, sikari, madara inda aka rarrarbawa al’ummar da basu da hali, da wadan da suke da nakasa, ma’aikata da kuma sauran jama’a.

“Makasudin yin haka shine don ayi kokari wurin rage wuya da tsanani da mutane ke fuskanta sannan su samu damar yin azumi cikin jin dadi da walwala.

Domin tabbatar da cewa anyi adalci wurin rabon wadan nan kayan abincin, gwamna ya bada umarnin hada kwamiti a cikin jaha da karamar hukumomi. Wannan kwamitin zai hada da mambas wadan da za a hada a dauko daga yan siyasa, yan kasuwa, shuwagabannin addini da masu unguwa.

Ya umarci wadan nan mambas da su fara aiki tare da yi masu gargadi akan yin murdiya da zata sa wasu al’umma su kasa samun wannan tallafi.

An samu labari daga masu yada labarai cewa kayan abincin sun hada da buhun shinkafa guda dubu sittin, buhun masara dubu hamsin, buhun wake dubu talatin, buhun sikari dubu goma da kuma katan katan din madara.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *