Labarai

Kunya ta kamaka, Fani-Kayode ya caccaki Buhari saboda sojojin Amurka sun zo har Najeriya sun ceto dan kasarsu da akai garkuwa dashi.

Spread the love

Femi Fani-Kayode ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da sojojin Najeriya bayan Sojojin Amurka sun ceto dan kasar su da ke Arewa a karshen mako.

DAILY POST ta ruwaito jiya cewa sojojin Amurka sun ceto wani Ba’amurke, mai shekaru 27, Philip Walton, wanda wasu mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da shi a Najeriya.

An koma da Walton zuwa arewacin Najeriya inda aka tsare shi kuma Pentagon ta tabbatar da cewa an aiwatar da aikin ne a ranar Asabar.

Da yake mayar da martani, tsohon Ministan na Sufurin Jiragen sama, ya yi wa gwamnatin Buhari ba’a, inda ya zarge ta da cewa tana da kyau wajen kashe ‘yan kasarta, yana mai ishara da harbin wasu masu zanga-zangar da ba su dauke da makami #EndSARS a yankin Lekki da ke Jihar Legas.

” A jiya ne dai Sojojin Amurka suka ceto wani Ba’amurke da aka yi garkuwa da shi a Najeriya a jiya, sun kashe wadanda sukayi garkuwa da shi su 6″.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button