Siyasa

Kuyi Hakuri Da Gwamnatina, Inji Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu.

Spread the love

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da hakuri da gwamnatinsa, yana mai cewa zai aiwatar da wasu ayyukan ci gaba don biyan bukatun al’ummarsa.

Bagudu ya fadi haka ne a jawabinsa na ranar dimokuradiyya da yayi a jiya.

Ya kara da cewa nasarorin da gwamnatinsa ta samu shi ne a bangaren noma, kiwon lafiya da ilimi, da kuma samar da ababen more rayuwa masu mahimmanci.

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da gudummawarsu ga ci gaban jihar ta kowace hanya da za su iya, yana mai kira garesu da su yaki yaduwar COVID-19 a cikin jihar ta hanyar bin duk ka’idojin da kwararrun likitocin suka ba su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button