Rahotanni

Kuyi Watsi Da Batun Kirkirar Wata Sabuwar Kasa A Tsakanin Najeriya Da Kamaru — CDD

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Wani Binciken Kwakwaf da Cibiyar Dimokradiyya da Samar da Cigaba ta Yammacin Nahiyar Afirka, ta Gudanar Ya Gano Cewar Labarin da Ake Ta Yadawa Akan Maganar Cewar Majalisar Dinkin Duniya Zata Kirkiri Wata Kasa a Tsakanin Najeriya Da Kamaru ba Gaskiya bane.

Cibiyar ta Sanar da Sakamakon Binciken natane a Shafukanta na Sada Zumunta dake Twitter, Facebook, WhatsApp Dakuma Sauran Dandulan Hukumar Dasuke a Yanar Gizo.

Ga Abinda Da Rahoton da Tafitar Yake Cewa :

“Shin Majalisar Dinkin Duniya Na Shirin Kirikirar Sabuwar Kasa Daga Kasashen Najeriya Da Kamaru?

Tantancewar CDD: Karya Ne!
Tushen Magana:
Majiyoyi da yawa sun wallafa rahotonnin dake cewa Majalisar dinkin Duniya zata kirikiri sabuwar kasa daga yankunan kasashen Najeriya da Kamaru a ranar 10 ga watan Yulin shekara ta 2020.
Sunan sabuwar kasar inji rahotannin zai kasance UN Organisation State of Cameroon.

Jaridar Guardian da ake wallafawa a Najeriya tace kirkiran wannan kasa zai kai Najeriya ga rasa kananan hukumomi 24 da Tsohon Shugaba Obasanjo ya sallamawa Shaugaba Paul Biya na Kamarun a baya.”

“Gaskiyar Magana:
Wannan batu babu gaskiya acikin tunda Majalisar Dinkin Duniya bata da yancin kirkiran wata kasa daga wassu kasashe dake wanzuwa.

Ita wannan kasa da aketa tababa akanta ta UN Organisation State of Cameroon bata cika sharudan da ake yiwa lakabi da the Montevideo Convention wanda suka bukaci cewa babu wata da take da yancin yiwa wata katsalidin acikin harkokinta na ciki ko wajenta.

Har wayau ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya bayyana rashin masaniyar sa game kirkiran sabuar kasar.”

“Wani rahoton shirin AIT Live ya bayyana tuntubar wata majiya daga Majalisar dinkin Duniya wanda tayi watsi da labarin kuma ta bayyana shi a matsayin na bogi ta kara da cewa Majalisar Dinkin Duniya bata kirkiran kasashe.”

“Shima da yake karyata labarin, Mr. Dahiru Bobbo, tsohon shugaban hukumar kula da iyakoki yace labarin labari ne na bogi.
Bobbo ya gayawa Francis Okoye na jaridar Leadership Newspaper cewa: “a iya sani na a matsayina na babban daraktan hukumar kula da iyakoki ta Najeriya tun daga shekarun 1999 zuwa 2006, ina tabbatar maka cewa babu wani taron tuntuba da ya gudana tsakanin Shugaba Obasanjo da Paul Biya tun daga farko zuwa karshen shekara ta 2003”
Dan haka babu wata yarjejeniya tsakanin kasa da kasa da take alamta cewa anyi musayen takardun yarjejeniya dan sallama wani yankunan kasashen Najeriya da Kamaru ga Majalisar Dinkin Duniya, inji Bobbo.

Bobbo yace tarurruka biyu Shugaba Obasanjo da Biya suka halarta kuma takardar bayan taro da aka fitar sun shafi kirkiro hukumar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Jamhoriyar Kamaru.
Kammalawa:
Rahotannin da ake yadawa cewa Majalisar Dinkin Duniya zata yanke kananan hukumomi 24 daga Najeriya dan kirkiran wata sabuwar kasa karya ne! CDD na shawartan jama dama kafafen yada labarai da su rika tantance labarai kafin yadasu.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button