Kwace Bizar Ganduje El Rufa’i Naji dadin kwace Bizar Azzalumai masu Magudin Zabe Saraki
Tsohon Shugaban Majalisar dattijan Nageriya Abubakar Bukola Saraki Ya Yabawa kasar Amurka Kan haramtawa wasu Yan Nageriya izinin Samun Bisar Shiva kasar inda ya rubuta a shafinsa na Facebook ya Mai cewa Na shiga cikin miliyoyin ‘yan Nijeriya don yabawa United Kingdom da sauran abokan tarayya na duniya Kan Batun haramta biza ga wasu masu kokarin lalata dimokiradiyyar Najeriya tare da hana su dukiyar ga masu lalata zaɓe. Ina kira ga Tarayyar Turai da itama ta bi sahu. Wannan ya zama dole a dauki mataki Kan masu ɓata mulkin demokraɗiyya a Najeriya abokan lalatattu ne a duniyar dimokiradiyya. Kuma Takunkumin ya kamata ya wuce ‘yan siyasa ya hada da jami’an zabe, jami’an tsaro da jami’an shari’a wadanda ke lalata dimokiradiyyarmu ta hanyar ayyukansu a lokacin zabe da bayansa.
Idan baku manta ba dai a jiya ne kasar Amurka ta bayarda sanarwar haramtawa wasu bizar Shiga kasarsu sakamakon zarginsu da Magudin Zabe wa’yanda aka haramtawa din sun hada da tsohon gwamnan Edo Adam Oshomale Gwamna Ganduje El Rufa’i da yahaya Bello na kogi da sauran su…