Labarai

Kwamitin Ayo Salami ya Bankado yadda Magu ya ci Amanar Shugaba Buhari.

Spread the love

A cikin Rahoton wucin gadi da Kwamitin da Mai Shara’a Ayo Salami ya Mikawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Rahoton Ya Nuna Ibrahim Magu Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na Hukumar EFCC ya Fi kowa cin Hanci da Rashawa a Najeriya.

Shugaba Buhari ya kafa Kwamiti karkashin Mai Shara’a Ago Salami domin Binciko Gaskiyar Zarge zargen da Akewa Ibrahim Magu, Wanda yayi Sana diyar Saukeshi daga Mukamin Shugaban Hukumar da Buhari yayi a watan da yagata.

Rahoton Kwamitin ya bankado Ibrahim Magu ya Karbi Makudan Kudade na Cin Hanci a Wajen Wasu Barayin Gwamnati domin Wankesu daga Zarge Zargen da Ake Musu.

Magu ya karbi Cin Hancin ta Hannun Abokansa, Masu Suna- Ahmad Ibrahim Shanono, mai kamfanin Chaja kudin kashen waje da Abokinsa Malamin Coci Pastor Emanuel Omale.

Da farko kwamitin ya binciki Pastor Omale menene tsakaninsa da Magu yace babu alakar komai Tsakaninsu Sai dai Magu yana zuwa Cocinsa yana masa Addu’a, sai dai da Bincike yayi Nisa An gano Kudi sama da Biliyan 100b a Asususun Pastor Inda yace Kudin na Magu ne wanda Ake Bashi Toshiyar baki Domin Dakatar da Bincikenda akewa Masu Laifi.

Shima, Ahmad Ibrahim Shanono wasu kamfanoni da gwamnati ta basu Aiki basu yiba, Sun kai Cin Hancin Biliyoyin Kudade ga Ibrahim Magu Inda ya Umarcesu da su Saka Kudin A Asusun Shanono.

Wasu Many an ‘Tan siyasa da Tsoffin Gwamnoni da dama sun Amsa kiran Kwamitin kuma su tabbatar da Shedun Baiwa Magu Cin Hancin Biliyoyin kudade ta asusun ajiyar Shanono Inji Kwamitin.

Idan Baku manta Ba a Shekarar 2014, lokacin da Farida Waziri ke Jagorantar Hukumar EFCC Ta Zargi Magu da Kwashe Fayil Fayil Na Masu laifi daga Ofishinsa yana kaiwa Gida ya boye Idan ya Amshi Na Goro a Hannun masu Laifi, wanda hakan ya Sanya Farida ta Dakatar dashi, har ma tanemi a Cireshi daga Hukumar ta EFCC a wancan Lokacin.

Har Ila Yau, a Shekarar 2015 lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo ya kai Sunan Magu gaban Majalisa domin su Tabbatar dashi a matsayin Shugaban Hukumar, Jami’an Tsaron DSS Sun Rubuta Takarda ga Shugaban Majalisar ba wancan lokacin Hon. Abubakar Bukola Saraki cewar Kar su amince da Magu domin Bai chancanci Shugabancin Hukumar ba, sun zargeshi da Aikata Cin Hanci Fiye da kima, Hakan ta Sanya Majalisa ta Ki amincewa dashi.

Duk da haka Osinbanjo ya Ce Magu yaci gaba da Zama a Hukumar har Sai Illa masha Allah, Lokacin Shugaba Buhari yana Jinya a Landan.

Magu dai ya zauna a Hukumar Har Tsawon Shekaru biyar a Hukuma a matsayin Rikon kwarya, Wanda hakan ya sabawa dokar kasa, Rikon kwarya a kowacce Hukuma ba’a wuce watanni shidda.

Ibrahim Magu dai yaron Ahmed Bola Tininbu ne, Kuma shi ya Kawoshi Hukumar, Wanda wasu mutane suke Tunanin ya kawo shi ne domin yayi amfani dashi A Siyasar shekara ta 2023 kan abokan Hamayyar sa ta Siyasa.

Jaridar Mikiya zataci gaba da kawo Muku Duk abinda Kwamitin Suka Bankado.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button