Rahotanni

Kwankwaso ne ya karbo belin Yunusa Yellow

Spread the love

Ga Dalilin Da Yasa Hukumomi a Jihar Bayelsa suka Sake Kama Yunusa Yalo Bayan Kwankwaso Ya Karbo Belinsa

Tun dazu nake ganin Hotunan wannan matashi Yunusa Yalo da Kuma Jagoran darikarmu ta Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa kwankwaso ana ta cewa da Kwankwason ke Kan madafun Iko da Yunusa Yalo bai tsinci kansa a wannan yanayi ba.

Bara nayi tariyar Baya kadan

Labarin Yunusa Yalo dai Labari ne da ya karade Jaridun kasar nan don haka ba a bukatar maimaitashi saidai wasu da yawa basu son menene dalilin komawarsa Jihar Bayelsa ba bayan kwankwaso ya karbo belinsa.

Abunda ya faru shine;

Wata Kungiyar Lauyoyi a Jihar Kano karkashin Barista Huwaila sune Suka fara kaiwa Yunusa Yalo Dauki a can Jihar Bayelsa bayan kamun farko da akayi Masa Kungiyar ta shiga ta futa domin ganin an bada Belin Yunusa Yalo Amma abun yaci tura daga karshe dai Alkali ya amince zai bada Belin Yunusa Yalo Amma akan wasu sharruda masu tsauri.

Kadan daga cikin sharudan shine Dole ne a samu Mutum uku su tsaya Masa 1 Babban ma’aikici a gwamnatin Tarayya 2 Babban basarake a Jihar Bayelsa 3 Babban Mutum Wanda ke da Gida a Jihar Bayelsa ko Babban birnin Tarayya Abuja, wadannan sharuda suna da matukar tsauri duba da yanayin Yunusa Yalo na Wanda yataho Bayelsa daga kauyen Kano domin yin Cirani, ana tsaka da wannan kiki-kaka sai Magana taje Kunnuwan Sanata Rabiu Musa kwankwaso lokacin Yana Kan Kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Kwankwaso shine ya cika dukka wadancan sharuda na beli aka saki Yunusa Yalo bayan an sakeshi Sanata Kwankwaso ya saya Masa sabon Babur me kafa uku(Keke Napep/Adaidaita sahu) ya bashi kyauta yace yaje ya nemi Abinchi.

Hukumomin Jihar Bayelsa sun sake damke Yunusa Yalo ne a karo na biyu bayan kin halarta kotu da yayi har sau biyu Wanda a doka hakan na nufin ya karya ka’idar Beli kenan Kuma Lokacin da akayi Masa kamu na biyun ana tsaka da Buga gangar siyasa ne Wanda Kowa ya sani duk wani Dan siyasa hankakinsa Yana Kan yakin Neman zabe ne hakan tasa Sanata Kwankwaso bai da masaniyar an sake Kama Yunusa Yalo Kai hatta Al’ummar Nigeria basu San an sake Kama Yunusa Yalo ba sai lokacin da asirin wasu Yan Kabilar Igbo ya tonu Wanda Suka sace Yara Yan Jihar Kano Suka maidasu Kirista tsawon shekaru hudu a lokacin ne Jama’a Suka tuna da abunda ya faru da Yunusa Yalo sannan Suka fahimci Ashe an sake kamashi.

Yau Alhamis 21 ga watan Mayu Alkali ya yankewa Yunusa Yalo Daurin shekaru 26 a Gidan yari Kan laifin da ake cewa ya aikata sai dai Alkalin ya bawa Yunusa Yalo damar daukaka Kara zuwa Kotun gaba. A wannan gabar ya zama wajibi muyi Kira ga gwamnatin Kano da Yan Majalisu na Jihar Kano da duk wani Mai fada aji a Jihar Kano musamman masu Mulki da su taimaka su kaiwa Yunusa Yalo Dauki domin sune hakkin kanawa ke kansu sune Bitalmalin kanawa ke hannunsu sune da Kujerar Mulki sune a hakku su kubutar da Yunusa Yalo. mai rubutu Khadija garba sanusi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button