Kwankwaso ya bayar da gudunmuwar gida kyauta domin kafa Cibiyar Bincike da da koyar da almajirai Ilimin Ci gaban Addinin Musulunci
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya bayar da rahoton cewa, cibiyar ta addinin Musulunci na da nufin samar da dama ga Almajirai da za su haddace kur’ani mai tsarki don horar da su tare da ba su shaidar kammala karatun firamare da sakandare da kuma shaidar difloma.
Ya ce, “Za su yi kwakkwaran horo a kan karatun Ingilishi da Larabci inda za su yi amfani da takardar shedar shiga jami’ar da kuma sanya sararin sama iyakarsu wajen neman ilimi.
Kwankwaso ya bayyana cewa cibiyar da aka assassa daga gidansa na Miller Road, daga yanzu ta Al’umma ce baki daya.
Ya kara da cewa cibiyar ra’ayinsa ce ta tabbatar da cewa tituna ba wai mabarata ba ne kawai, har ma wadanda ake gani suna bara a samar musu da damar rayuwa.
“Wannan cibiya ita ce a yi wa mutanen da suka haddace Al-Qur’ani rajista, su zabi wadanda suka cika sharuddan sannan a duba su.”
“Tana da manhajar karatu da za a horas da maza da mata cikin kankanin lokaci domin su samu shaidar kammala firamare da sakandare.
“Za a ba su takardar shaidar karatun addinin Musulunci. Da wannan za su iya zuwa Jami’o’i kuma sararin sama zai zama iyaka a gare su. Za a ba su dama don a ba su takaddun shaida da kuma ba su masauki a cikin tsarin,” inji shi.