Labarai

Kwarai da gaske nine nace Muna bukatar a Chanja Sunan Maryam Shetty ~Cewar Ganduje.

Spread the love

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan dalilan da suka sanya aka cire sunan Maryam Shetty daga cikin sunayen ministocin da suka fito daga jihar Kano. A cikin satin da ya gabata ne dai Shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar dattawa takardar cire sunan Dr. Maryam Shetty daga cikin ministocin da za a tantance inda ya maye gurbinta da Dr. Mariya Mahmud Bunkure.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasan a yayin wata tattaunawa da Leadership Hausa, ya bayyana cewa ba da saninsu aka sanya sunan Maryam Shetty ba a cikin jerin ministocin da suka fito daga jihar Kano.

Ganduje ya bayyana cewa wasu ƴan gutsiri tsoma da ƴan bani na iya ne na fadar shugaban ƙasar suka saka sunan Maryam Shetty a cikin sunayen ministocin, ba tare da an tuntuɓe su ba.

Kasan a fada akwai ƴan bani na iya, kasan a fada akwai ƴan gutsiri tsoma, wannan suna sai dai muka ganshi kawai daga sama. Amma tunda mun san shugaban ƙasa yana da ikon yin hakan, mu kuma mabiyansa ne, kuma mun san a dimokuraɗiyya sai ka bi a hankali, sai ka yi haƙuri, saboda haka sai ba mu ce meyasa aka yi haka ba.

Na farko dai ba mu santa sosai ba, bamu ma santa ba, to tunda ba mu santa ba bamu da ma’auni da za mu ce za ta iya wannan aiki ko ba za ta iya ba. To amma inda gizo ke saƙar shi ne batun soshiyal midiya. Soshiyal midiya nan kana zato ka yi abu ba wanda ya sani, wataƙila ma kai da ka yi abun an fika sanin ka yi.” “Soshiyal midiya suka fara fitowa suna cewa wannan mai ta alaƙanta da za ta iya riƙe wannan mulki, kuma yanzu mutanen Kano har ma ta kai irin wannan ce za ta wakilci mutanen Kano. To wannan sai ya kawo damuwa. Kaga damuwar nan ba daga Ganduje ta zo ba, ba daga sauran al’umma ta zo ba, damuwa ta zo daga al’umma waɗanda su ke da hange kan wannan lamari.

Ganduje ya bayyana cewa wannan damuwar da aka nuna ta je kunnen shugaban ƙasa, wanda ya tambaye shi ko shi ne ya sanya sunanta, inda ya ce sam baya da masaniya kan yadda aka yi sunanta ya shiga cikin ministocin. Shugaban na APC ya yi bayanin cewa hakan ya sanya Shugaba Tinubu ya shawarce shi kan sauya sunan Maryam Shetty, inda shi kuma ya bayar da goyon bayan a cire sunanta, domin ba wacce ta fi ta cancanta ta riƙe muƙamin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button