Labarai
Kyakkyawan Albishir Ga Ma’aikatan N-Power..
Muna Kokarin Biyan Ma’aitan N-Power Da Akayi Wata Uku Ba A Biyasu Ba, Inji Minista Sadiya.
Ministan agaji, da cigaban jama’a, Sadiya Farouk ta bayyana cewa kusan masu amfani da N-Power 12,000 har yanzu ba a biya su bashin watanni uku ba.
Ministar ta ce jinkirin ya faru ne saboda wasu matsaloli da suka Fuskanta, kuma nan ba dadewa ba za a magance su.
Ministar ta kara da cewa ma’aikatarta tana aiki tare da ofishin Babban Asusun Tarayya don warware matsalolin biyan.