Labarai
Labarai: Sojoji, da ‘yan sanda suma ‘yan Nigeria ne kuma suna kishi. Inji Garba Shehu. Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya- cewar Sojin Najeriya.
- A rana guda mutane 3700 suka mutu a Amurka saboda corona.
. - Kungiyar Izala ta umurci limamai su fara Al’qunuti yayin Khamsu Salawat saboda rashin tsaro.
. - Kwamishina Gettado na jihar Gombe ya bayyana yadda suka jagoranci wakilan gwamnatin tarayya don bunkasa yankin Zangewawa da ya hada Karamar hukumar Funakaye, da Dukku, da Kuma Kwami, za a yi aiki na musamman ne da zimmar bunkasa noma, da kiwo a yankin.
. - Rufe makarantu a Arewa tamkar mika wuya ne, da kuma sallamawa ‘yan bindiga – Inji jama’ar arewa, inda har ta kai ga a Kano an yi zanga-zanga da gwamnati tace ta rufe makarantu, a cewar su yanzu ma Arewar ce koma baya a bangaren ilimi a kasar.
- Sojoji, da ‘yan sanda suma ‘yan Nigeria ne kuma suna kishi. Inji Garba Shehu.
- Idan Gwamnati ba zata iya kare al’umma ba tace ba zata iya ba kawai, sai ace al’umma su kare kansu- inji Dr. Mairo Mandara
- Gwamnan jihar Kaduna ya ce za su dinga bibiyar mutane idan ba sa bin ka’idar corona zai rufe jihar kif.
- Gwamna Masari na jihar Katsina ya ce yaran makarantar Kankara a hannun ‘yan bindiga suke, ba a hannun boko haram ba, sai dai shekau ya ce a hannun shi suke. ko waye mai gaskiya a cikin su? Lokaci ne zai tabbatar.
.
*Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya-/Sojin Najeriya.
. - Gwamnatin Najeriya ta ce za ta soke daukacin layukan waya na wadanda ba su da shaidar zama dan kasa NIN.
- Shugaba Buhari ya cika shekaru 78 a yau.
- ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan kasuwa uku a Zamfara bayan sun karbi miliyan 6.
*Ibrahim Garba Wala ya shaidar da yadda aikin ‘yansanda yake gurbacewa saboda cin hanci, da rashawa. Ya kirayi Shugaba Buhari yasan da hakan.
.
- ‘Yan kungiyar IPOB sun sha alwashin kare al’ummar yankin su na Igbo saboda tabarbarewar lamuran tsaro a Najeriya musamman da aka sace dalibai a makarantar Kankara ta jihar Katsina.
- Gwamnatin Najeriya ta ce kwalliya ta biya kudin sabulu a rufe boda a Najeriya, inda a yanzu take shirin bude bodar.
Karshen kanun labaran kenan sai a dakaci na gaba in shaa Allahu.
Daga Bappah Haruna Bajoga.