Ƴan Najeriya suna tambayar mawaƙi Rarara kuɗin su daya amsa domin rerawa Buhari waƙar jinjina da yabo.

Ƴan Najeriya suna tambayar mawaƙi Rarara kuɗin su daya amsa domin rerawa Buhari waƙar jinjina da yabo.

Idan za’a iya tunawa tun a watan Satumba na shekarar 2020 ne, shahararren fasihin mawakin nan na siyasa wanda akafi sani da Dauda Kahutu Rarara yayi alƙawarin fitowa da wata waka ta musamman domin zayyana ayyuka na musamman da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi wa Najeriya.

To amma sai dai kimanin watanni shida kenan, shiru kake ji kamar maye yaci shirwa.

Inda Rarara yayi luƙum dashi, kai kace jama’a masoya basuyi masa goma ta arzikin kuɗi a wannan account din ba.

Account Name: RaraRa Multimedia Company Nig Ltd

Account No:1016422103

Bank: Zenith Bank

Mawakin na Baba Buhari wanda ya daɗe yana bayar da gudummawa a tafiyar APC dama kafuwar Gwamnatin APC a Nigeria, yayi shiru, ko tunanin sa mutane sun manta ne? ko kuma ruwa ne ya ƙare wa ɗan kada?

Rarara har  bayyanawa mutane cewa yayi, ya tanadi wata sabuwar waƙa ta musammam da zai ƙaddamar da ita, duk da cewa yana da hali da wadatar da zai iya ɗaukar nauyin aikin waƙar gaba ɗaya, amma don samar da sabon yanayin da zai ƙarawa masoya Baba azama da ƙaimi, ya amshi ƴan mutsabbansa a cika Aljihu.

A cewar Rarara a wancan lokacin, ya tsara hakan ne, don ƙara fitowa da duniya cewa Shugaba Buhari yana nan tare da masoyansa.

Inda daga ƙarshe ya nemi da kowanne masoyin Shugaba Muhammadu Buhari daya tura da naira duba ɗaya ta account number ɗin sama.

Tabbas ƴan Najeriya, basa mantuwa, domin kuma bayan kimanin wata shida da gaza fito da wannan waƙar, mutane sun soma tambaya.

Ga kaɗan daga cikin kalaman su, domin waƙa a bakin mai ita tafi daɗi.

“Ya kamata Ku maka shi a KOTU tunda ya yaudareku, ya karbi kudinku baiyi abinda kuka sashi yayi ba”.

– Ashiru Tanko

“Hhhhhhh Ai idan ba ai sharan masallaciba ayi na kasuwa.

Suwaiba Ibrahim

“Naturamar 3000 dazai biyanma danacika nasiyawa yarinyarnan ABAYA dashi tadameni ”.

Muhammad Ibn Abdullahi

IN BAI MAIDOMAN DUBU TABA TO XAMU HADU GABAN Allah”.

-Zainab Isyaku.

Haƙika a hazaƙar mawaki Rarara mutane sun yi zaton kafin a gama danƙara masa kuɗi a asusun bankin sa da ya rarraba ana loda masa kudi a ciki, za a wayi gari ne Najeriya ta ɗauka ana ta shagali da sauraren waƙar sai aka ji shiru kusan shekara ɗaya kenan bai ce komai a kai ba ya ja bakin sa yayi shiru, bayan ya ji miliyoyi a aljihun sa.

Yan Najeriya na neman bayani ko kuma waƙa Rarara.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *