2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

Aminu Saidu, wani bakano dan shekara 35 da ke neman takarar shugaban kasa, a ranar Alhamis, ya bayyana niyarsa na neman takarar neman kujerar shugaban kasar Nigeria sannan ya nemi taimakon fitaccen dan wasan kwallon kafa Ahmad Musa, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar matashin mai neman takarar, gabanin babban zaben shekarar 2023, ya ce ya yanke shawarar fara neman tallafi ne daga kowanne sashi da ke taka muhimmin rawa wurin cigaban kasa.

“A matsayina na matashi dan Nigeria da ke fatan zama shugaban kasa a 2023; yana da muhimmanci in fara tuntubar matasa na gida da waje kamar irinsu Ahmed Musa don neman shawara da tallafi,” in ji shi.

Matashin mai neman takarar ya kara da cewa matasan Nigeria na da muhimmin rawa da za su taka wurin tabbatar da cewa Nigeria ta cigaba a kowanne bangare.

A bangarensa, Ahmed Musa ya ce ziyarar da matashin dan takarar Aminu Sa’idu ya kai masa a matsayin mataki mai kyau a kuma lokacin da ya dace.

Idan za a iya tunawa, Aminu ya bayyana niyarsa na takarar shugabancin kasa tun farkon wannan shekarar yana mai alwashin amfani da damar dokar ‘not too young to run’ da aka yi wacce ta rage shekarun masu shiga takara.

Daga Ahmad Aminu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *