Labarai

2023: Atiku zai lashe zabe da rinjayen kuri’u milyan bakwai ~Cewar Ayu shugaban PDP na kasa.

Spread the love

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiorcha Ayu, ya bayyana cewa dan takararsu na shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai firgita ‘yan Najeriya a zaben 2023, inda zai yi nasara da kuri’u miliyan bakwai.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Laraba a dakin wasanni na cikin gida da ke Bauchi.

A baya Atiku ya karbi bakuncin dubban masu sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress da sauran jam’iyyun siyasa, a wani biki da aka gudanar a wannan rana a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Abubakar yana gefen abokin takararsa, Ifeanyi Okowa; shugaban jam’iyyar na kasa, Iyiorcha Ayu; Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Darakta Janar na Majalisar Yakin Neman Zaben sa Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo.

Gwamnonin Bauchi, Bala Mohammed; Adamawa, Umaru Fintiri da na Taraba, Darius Ishaku, da mataimakansu sun halarci taron.

Tsoffin gwamnonin Jigawa, Sule Lamido; Adamawa, Boni Haruna da Gombe, Ibrahim Dankwambo; tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; da sauran manyan baki, su ma sun halarta.

Sai dai babu daya daga cikin gwamnonin da jiga-jigan jam’iyyar PDP masu biyayya ga Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da ya halarci taron.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button