Labarai

Labarai: Sojoji, da ‘yan sanda suma ‘yan Nigeria ne kuma suna kishi. Inji Garba Shehu. Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya- cewar Sojin Najeriya.

Spread the love

  • A rana guda mutane 3700 suka mutu a Amurka saboda corona.
    .
  • Kungiyar Izala ta umurci limamai su fara Al’qunuti yayin Khamsu Salawat saboda rashin tsaro.
    .
  • Kwamishina Gettado na jihar Gombe ya bayyana yadda suka jagoranci wakilan gwamnatin tarayya don bunkasa yankin Zangewawa da ya hada Karamar hukumar Funakaye, da Dukku, da Kuma Kwami, za a yi aiki na musamman ne da zimmar bunkasa noma, da kiwo a yankin.
    .
  • Rufe makarantu a Arewa tamkar mika wuya ne, da kuma sallamawa ‘yan bindiga – Inji jama’ar arewa, inda har ta kai ga a Kano an yi zanga-zanga da gwamnati tace ta rufe makarantu, a cewar su yanzu ma Arewar ce koma baya a bangaren ilimi a kasar.
  • Sojoji, da ‘yan sanda suma ‘yan Nigeria ne kuma suna kishi. Inji Garba Shehu.
  • Idan Gwamnati ba zata iya kare al’umma ba tace ba zata iya ba kawai, sai ace al’umma su kare kansu- inji Dr. Mairo Mandara
  • Gwamnan jihar Kaduna ya ce za su dinga bibiyar mutane idan ba sa bin ka’idar corona zai rufe jihar kif.
  • Gwamna Masari na jihar Katsina ya ce yaran makarantar Kankara a hannun ‘yan bindiga suke, ba a hannun boko haram ba, sai dai shekau ya ce a hannun shi suke. ko waye mai gaskiya a cikin su? Lokaci ne zai tabbatar.
    .
    *Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya-/Sojin Najeriya.
    .
  • Gwamnatin Najeriya ta ce za ta soke daukacin layukan waya na wadanda ba su da shaidar zama dan kasa NIN.
  • Shugaba Buhari ya cika shekaru 78 a yau.
  • ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan kasuwa uku a Zamfara bayan sun karbi miliyan 6.

*Ibrahim Garba Wala ya shaidar da yadda aikin ‘yansanda yake gurbacewa saboda cin hanci, da rashawa. Ya kirayi Shugaba Buhari yasan da hakan.
.

  • ‘Yan kungiyar IPOB sun sha alwashin kare al’ummar yankin su na Igbo saboda tabarbarewar lamuran tsaro a Najeriya musamman da aka sace dalibai a makarantar Kankara ta jihar Katsina.
  • Gwamnatin Najeriya ta ce kwalliya ta biya kudin sabulu a rufe boda a Najeriya, inda a yanzu take shirin bude bodar.

Karshen kanun labaran kenan sai a dakaci na gaba in shaa Allahu.

Daga Bappah Haruna Bajoga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button