A daidai Lokacin da aka sace dalibai 200 ka Kuma kashe 13 Shi Kuma Gwamnan Niger ya tsallake Zuwa kasar waje.

‘Yan sa’o’i kadan bayan sace daliban da yawa daga makarantar Islamiyya ta Saliu Tanko a ranar Lahadi, Gwamnan Jihar Neja, Sani Bello, ya bar Najeriya.

A cewar hadiminsa, Mary Noel-Berje, Mista Bello ya yi tafiya zuwa kasashen waje domin gudanar da aikin neman hanyoyin magance matsalolin tsaro a jiharsa.

“Gwamnan, wanda ya bar kasar don binciko duk wasu hanyoyi na karfafa gine-ginen tsaro na jihar kafin lamarin ya faru, ana sa ran dawowa ba da jimawa ba,” inji ta.

Ta kuma bayyana cewa gwamnan ya bayar da umarni ga jami’an tsaro da jami’an gwamnatin jihar da su yi duk abin da za su iya wajen ganin an dawo da yaran Tegina Islamiyya da aka sace da sauransu.

“Gwamnan, wanda ake sa ran dawowa kasar cikin kankanin lokaci, ya bada tabbacin ceto da kuma dawo da yaran cikin koshin lafiya.”

“Gwamna Sani Bello ya kuma tabbatar wa da dukkan‘ yan Neja cewa gwamnati za ta ci gaba da yin duk abin da za ta iya don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar tare da ba da tabbacin ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali na jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *