A Gaggauce l Masu Garkuwa Da Mutane Sun Yi Garkuwa Da ‘Dan Tsohon Sarkin Kano

An sace Dan Wan tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi a hanyar Abuja Zuwa Kaduna.

An rawaito cewa an yi garkuwa da Aminu Musa Abdullahi, dan wa ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da aka tsige.

Jaridar Dailytrust ta rawaito cewa an sace Abdullahi, wanda aka fi sani da Yaya Baba yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.

Wata majiya ta fada wa jaridar cewa masu garkuwan sun tuntubi danginsa don neman kudin fansa, amma ba su bayyana kudin ba.

Majiyar ta ce;

“Iyalan sun samu kudin da aka nema kuma tun daga lokacin da aka bawa wanda zai kai kudin ga masu garkuwar don a sako Shi, basu kara jin duriyarsa ba. Har zuwa yanzu, ba su yi magana da iyalin ba.”

Ubangiji Allah ya fitar da shi da sauran al’umma da su ke hannun wadannan azzalumai a duk inda su ke.

Daga:- Aliyu Adamu Tsiga

Leave a Reply

Your email address will not be published.