A Zaben 2023 Muna shirya Hanyar da zamu kifar da APC da PDP a Nageriya ~Inji Jega

Gabanin babban zaben shekarar 2023, jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta fara kamfe na ganin ta hada kan masu ruwa da tsaki game da kafa wata babbar jam’iyya wacce za ta zama babbar mafita ga manyan jam’iyyun siyasa biyu na kasar.

Jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) sune manyan jam’iyyu biyu a kasar.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, ya ce an gudanar da gangamin ne da nufin kawo dukkan masu fada a ji a sabanin siyasar ubangida da ake yi a sauran jam’iyyun siyasa.

Jega, tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya ce bautar ubangida ta yi mummunar illa ga siyasar kasar.

Ya ce tare da sabon yanayin da ke faruwa a jam’iyyarsa da kuma yadda ake tafiyar da hada-hada a duk fadin kasar, yana da kwarin gwiwar cewa PRP za ta samar da kyakkyawan zabi ga ’yan Najeriya.

Dangane da burinsa na 2023, Jega ya ce lokaci ya yi da za a yi magana game da burin kowane mutum, yana mai cewa idan aka bar kishi na siyasa ya hau kan gaci, manufofin jam’iyyar da suke aiki a kansu na iya wargajewa.

“Muna sake kirkirar jam’iyyar ta hanyar kawo dukkan masu ruwa da tsaki a cikin jirgin, saboda haka aka shirya wannan taron tattaunawa don masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kebbi.

“Muna kokarin gina wata sabuwar hanyar siyasa gabanin 2023 kan manyan jam’iyyun siyasa biyu a kasar,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *