Labarai

Abin Haushi: Wani Ɓarawo A Abuja ya siyar da wayar wutar lantarkin da ya sata ta Naira miliyan ɗaya akan Naira dubu ɗaya kacal

Spread the love

A yayin binciken ‘yan sanda, wanda ake tuhumar ya amsa laifin satar, kuma ya ce ya sayar wa Fahat Aliyu wayar, a kan Naira 1,000 kacal, kamar yadda lauya mai shigar da kara ya shaida wa kotu.

Wani da ake zargin barawo ne Awal Abdullahi ya saci kebul na lantarki da ya kai Naira miliyan daya a wani katafaren gida da ke Abuja ya sayar da ita kan Naira 1,000.

A yau Alhamis ne wata kotun yanki mai daraja ta daya da ke Dei-Dei a Abuja ta fara sauraren karar.

Mista Abdullahi, mai shekaru 30, yana fuskantar shari’a kan aikata laifuka da kuma sata.

Dan sanda mai shigar da kara, Chinedu Ogada ya shaida wa kotun cewa mai shigar da kara John Behora na unguwar Sunshine Estate Gwarinpa Abuja ya kai rahoton satar a ranar 30 ga Disamba, 2022.

Mista Ogada ya ce wanda ya shigar da karar ya yi zargin cewa a ranar 28 ga watan Disamba, wanda ake tuhumar ya shiga cikin gidan da akaiyi laifin da wayo ba tare da amincewar masu shi ba ya kuma kwashe wayar gidan.

Daga baya an kama Mista Abdullahi aka mika shi ga ‘yan sanda.

A yayin binciken ‘yan sanda, wanda ake tuhumar ya amsa laifin satar, kuma ya ce ya sayar wa Fahat Aliyu wayar, a kan Naira 1,000 kacal, kamar yadda lauya mai shigar da kara ya shaida wa kotu.

Ya ce wanda ake kara ya kara shaida wa ‘yan sanda cewa a wani lokaci da ya wuce ya saci sandar karfe a gidan ya sayar wa Aliyu kan Naira 1,200.

Laifukan sun ci karo da tanadin sashe na 343 da na 288 na dokar Penal Code, in ji Mista Ogada.

Mista Abdullahi, ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Alkalin kotun, Saminu Suleiman, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Mista Abdullahi a gidan yarin da ke Suleja, har zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu domin sauraren karar.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button