Labarai

Abinda A’isha Bichi ta yiwa Abba Gida-Gida ya nuna Bata da tarbiya hakan ya nuna ita ba matar Arziki bace ~Cewar Fahad Ibrahim Danladi mazaunin Amurka.

Spread the love

Fahad Ibrahim Danladi Dan asalin jihar kano ya rubuta hakan ne a shafin sa na Facebook Yana Mai cewa Gaskiya abinda Aisha Bichi ta yiwa Abba Kabir a airport din Kano ya nuna ba ta da tarbiya, sannan hakan ya nuna ita ba matar arziki ba ce. Irin wannan rashin mutuncin da masu madafun iko keyi yasa mutane ke daukan doka a hannun su har takai sun dauki makamai.

Saura wata biyar ku sauka mu hau, idan mun saka KNUPDA ta rushe gidan su ko na dangin ta, su fara kuka. 

Allah yasa mufi karfin matan mu amma dai shi wannan bawan Allah din Allah ya jarabce sa.

A jiya ne rikici ya faru tsakanin Dan takarar Neman Gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyar NNPP Engr Abba Kabir Yusuf da Aisha Bichi matar daractan DSS na Kasa a filin jiragen sama na malam Aminu Kano lamarin Daya jawo Cece kuce a kafafen SADA zumintar zamani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button