Abu biyar da yakamata ka sani a yau

Jami’ar Abuja (Uni Abuja) ta kori dalibai arba’in da shida saboda rashin da’a


Majalisar Dattawan makarantar Jami’ar Abuja ta kori  Dalibai na Jami’ar saboda hannu a cikin wasu ayyukan rashin da’a 
 Shugaban yada labarai da alakar jami’a, Dr Habib Yakoob, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi, talatin ga watan Mayu.  Yakoob ya bayyana cewa rashin da’a ya jawo hakan.

Likitoci mazauna sun tsawaita wa’adin yajin aiki da makonni biyu

Kungiyar Likitocin Kasa (NARD) ta tsawaita yajin aikin ta na tsawon makonni biyu ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihohi don magance matsalolin mambobinsu a duk fadin kasar 
Wannan sabuntawar na kunshe ne a cikin sanarwar bayan taro a karshen taron kungiyar karo na arba’in da daya (OGM) wanda aka gudanar a Nnewi / Awka, Anambra, tsakanin ashirin da biyar ga Mayu zuwa ashirin da tara ga Mayu.

An ba da rahoton harbe tsohon mai ba Goodluck Jonathan shawara a Owerri

An ba da rahoton harbe tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak a Owerri, jihar Imo 

wasu ‘yan bindiga sun kashe shi a daren ranar Asabar, a cewar wani rahoto da jaridar Leadership ta ruwaito.  Littafin ya kuma bayyana cewa Umar Ardo, wani jigo a jam’iyyar (PDP) kuma aminin Mista Gulak, ya tabbatar da kisan.

Gobara ta kone Kasuwar kayayyakin gyara ta Ladipo

Gobara ta kama bangaren Alapeju na kasuwar Ladipo a yankin Mushin da ke Legas a ranar Lahadi, talatin ga Mayu
Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas da suka isa wurin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi.

‘Yan bindiga sun cinnawa sabon ofishin INEC wuta a Imo

Sabon ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) an cinna masa wuta a garin Okwudor da ke cikin Karamar Hukumar Njaba ta Jihar Imo 
 A cewar INEC, an kona ofishin ne da misalin karfe sha daya da rabi na safiyar Lahadi, talatin ga watan Mayu.

kwamishinan zaben na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu zabe, Festus Okoye, ya ce harin na baya-bayan nan ya sanya adadin ofisoshin INEC arba’in da biyu da aka kai wa hari a fadin kasar.  

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *