Abubuwa sun tabarbare yanzu, har ana kayyadewa Soji harsashin da zai rike inji Sanata Ndume

Ali Mohammed Ndume, Sanata mai wakiltar mutanen Borno ta Kudu ya bayyana cewa abubuwa basu tafiya yadda su ka kamata a yakin Boko Haram.

Sanata Ali Mohammed Ndume ya ce lamarin har ya kai ana ware adadin harsashin da ake ba sojoji.

The Cable ta ce ‘dan majalisar ya yi wannan bayani ne a ranar Talata a garin Abuja, inda ya yi kira ga hukuma su inganta halin da jami’an tsaro suke ciki.

Jaridar ta rahoto Ali Mohammed Ndume ya na cewa sojoji sun saba da wannan tsari na kayyade masu yawan harsashin da za su fita zuwa filin daga da su.

“Ba a taba yin lokacin da abubuwa su ka tabarbare mana ta ko ina irin wannan lokaci ba. Lamarin ya lalace ta yadda an koma yin sulhu da ‘yan bindiga.”

“A Shiroro, mazauna gari sun yi sulhu da ‘yan bindiga, aka ba su damar su zauna lafiya. Yau a Najeriya, mu na da wasu masu iko a cikin gwamnatinmu.”

“Idan muka tunkari jami’an sojoji a kan ‘me yake hana ku aiki?’ sai su ce mana ‘ba mu da kudi’; muna lallaba abin da mu ka samu ne.” inji Sanata Ndume.

“Ina magana da jami’an tsaro a kai-a kai. Abin ya kai inda ya kai, sojojin kasa suna kayyade harsashi. An saba wannan, a raba harsashin da za ayi aiki da su.”

“Za a iya cewa ni na fada.” Sanatan ya na mai bada tabbacin zancensa, ya ce: “Na zagaya dakarun sojoji; ban ga wani soja da sabuwar bindigar AK-47 ba har yau.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *