Labarai

Aisha Buhari: Kungiyar Ɗaliban Najeriya ta ayyana zanga-zanga a fadin kasarnan saboda tsare Aminu Muhammad

Spread the love

Shugaban kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ya sanar da gudanar da zanga-zanga a fadin kasarnan sakamakon kamawa da tsare mamban kungiyar Muhammad Aminu Adamu.

Jami’an tsaro da ake kyautata zaton jami’an ‘yan sandan sirri ne, SSS ne suka kama Mista Muhammad, wanda dalibi ne a shekarar karshe a Jami’ar Tarayya Dutse, a makon jiya.

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ce ta bayar da umarnin kama shi kan wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter inda ya bayyana cewa uwargidan shugaban kasar ta zama mai kiba da kudin talakawa.

Sai dai an gurfanar da shi a asirce a wata babbar kotun Abuja a ranar Laraba inda aka bayar da umarnin tsare shi a gidan yari na Suleja.

Sai dai NANS a wata sanarwa da ta fitar a ranar 1 ga watan Disamba ta yi tir da halin da Mista Muhammad ya shiga.

“Sakamakon gajiyar da mukai da duk wasu hanyoyin da muke da su kafin fuskantar neman ‘yancin daya daga cikin mu da aka kama da azabtarwa, da cin zarafi, da tsare shi da jami’an gwamnati suka yi, ana sanar da ku shawarar da kungiya ta yanke. Shugaban kungiyar daliban Najeriya na kasa ya ce a cigaba da gudanar da zanga-zanga a fadin kasarnan,” sanarwar da Usman Barambu, shugaban NANS ya sanya wa hannu.

“Mun tuntubi kuma mun hada kai kuma ba mu samu sakamako mai kyau ba wajen neman ‘yancin Aminu Adamu Muhammad, dalibin Jami’ar Tarayya Dutse. Don haka za a fara zanga-zangar kamar haka.”

NANS na shirin fara zanga-zangar ta a fadin kasarnan a ranar Litinin 5 ga watan Disamba, domin neman a saki Mista Muhammad ba tare da wani sharadi ba.

Sassan sanarwar sun ce “muna zanga-zangar adawa da Sufeto Janar na ‘yan sanda ne; Usman Alkali Baba da matar shugaban kasa; Aisha Muhammadu Buhari.”

NANS tana ƙarfafa membobinta a duk faɗin ƙasarnan da su nuna ƙarfinsu don yaƙar kowane nau’i na rashin adalci a yanzu saboda “rauni ga mutum rauni ne ga kowa.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button