Aisha Buhari Ta Kaddamar Da Sabon Gangamin Yaƙi Da Rashin Tsaro.

Uwar gidan shugaban Nijeriya Aisha Muhammadu Buhari, ta ƙaddamar da wani sabon gangamin yaƙi da rashin tsaro a Arewa.

Gangamin mai taken #ArewaMufarka, ta ƙaddamar da shi ne a shafinta na Twitter ɗauke da wasu hotunan mutane da ke rike da allunan rubutun kira da a kawo ƙarshen rashin tsaro da satar mutane.

A ranar Asabar ne dai ta ƙaddamar da wani gangami mai taken #Achechijamaa, wanda ya janyo cecekuce, kafin daga bisani ta sake ɓullo da wannan gangami na #ArewaMufarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.