Labarai

Ajiyar jam’iyar APC na bawa Gwamna Bello Kuma idan na dawo nageriya zan karbi abata ~ Cewar Gwamna Mai mala.

Spread the love

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe na shirin dawowa a matsayin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC da zarar ya dawo daga jinya kamar yadda wasikar da ya fito daga jam’iyyar APC ta bayyana.

Wasikar mai dauke da kwanan watan Fabrairu 28, 2022, wacce jaridar PUNCH ta samu, an aikewa Gwamna Sani Bello na jihar Neja da sauran mambobin kwamitin riko kafin tafiyar tasa.

A cikin wasikar tana nuni da cewa Buni da son ran sa ya mika mulki ga Bello.

Wasikar ta karanta a wani bangare na cewa, Ina sanar da ku cewa, zan kai ziyarar aikin jinya zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa dubai daga yau 28 ga Fabrairu, 2022. Zan Kuma zan dawo na ci gaba da aiki bayan an sallame ni daga asibiti.

“Idan ba ni ba, ina mika muku ayyukan ofishina a matsayin Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Musamman na Kasa na Riko a jam’iyarmu ta APC na rubuta wannan ne don baiwa kwamitin damar kammala duk shirye-shiryen da za su kai ga taron kasa da aka shirya yi a ranar 26 ga Maris, 2022, da sauran ayyukan da ofishin zai buƙaci.

“Ina gayyatar dukkan membobin kungiyar da su ba Gwamna Abubakar Sani Bello hadin kai ta hanyar ba shi dukkan goyon bayan da na samu daga gare ku.”

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Laraba ya bayyana cewa, duk da cewa Buni ya mika mulki ga Bello, nan da nan suka gano cewa kwamitin Buni ba shi da wani shiri na gudanar da babban taron na ranar 26 ga Maris.

El-Rufai ya ce an sanar da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), kuma ya ba da umarnin a gaggauta daukar Bello kan harkokin jam’iyyar na dindindin.

Gwamnan ya ce Buni ba zai dawo a matsayin shugaban kwamitin riko ba, ya kara da cewa akalla gwamnoni 19 ne ke goyon bayan Bello.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button