Allah Daya Gari Bam-Bam: Ahalin Obama sun shiga makoki da alhinin mutuwar karen su.

Rayuwar kare a nahiyar Turai da yammacin duniya wani abune mai daraja, wanda karnuka suka kasance cikin karamci, aminci, da kuma soyayya maras iyaka.

Wannan shine yasa, kafatanin iyalin Obama, tsohon shugaban ƙasar Amurika, suka tashi cikin alhinin mutuwar karen da suka jima dashi.

Karen mai ratsin fari da baƙi, kare ne ɗan ƙasar Portugal, wanda suka sanya masa suna da “Bo”.

Matar Obama, wato Michelle Obama, itace ta faɗi mutuwar Bo, lokaci kaɗan bayan ya mutu murus, inda ta tabbatar da cewa, cutar daji (Cancer) itace Ummul aba’isin mutuwar tasa.

Idan za’a iya tunawa wa, Bo ya shiga cikin rayuwar iyalan Obama ne tun a Aprilu na shekarar 2009, wato wata uku kenan cif cif bayan Obaman ya shiga fadar White House.

Ko daga ɓangaren Obama, sai daya saka tsohon hotonsa da karen sanda yake raye, inda ya rubuta wani saƙo mai ban tausayi a ƙasa, domin nuna bankwana da Bo.

Allah Daya Gari Bam-Bam: Ahalin Obama sun shiga makoki da alhinin mutuwar karen su.
Bo

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *