
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya bayyana cewa, duk da yake shi ba dan siyasa ba ne, amma ya zama wajibi su cigaba da yin addu’o’in samun nasarar Jam’iyya APC mai mulkin Nijeriya, domin ganin ta cigaba da mulki har nan da shekaru 32, kamar yadda ya ji wasu suna ta fatan faruwar hakan.
Sarkin Dauran ya bayyana haka ne a gidan Gwamnatin Jihar Katsina jiya lokacin da ya kai wa Gwamna Aminu Bello Masari ziyarar jaje dangane da iftila’in gobarar Babbar Kasuwar Katsina.
“Masarautar Daura tana da abubuwa guda biyu; Shugabancin kasar nan yana hannun mutumin Daura, haka Gwamna Masari shi ma dan Daura ne, dukkansu kuma adalan shugabanni ne. Ya zama wajibi mu dage da addu’o’i ba dare ba rana na ganin sun yi nasara a cikin wannan mulki nasu,” inji Mai Martaba Sarkin.
Alhaji Faruk Umar ya kara da cewa, “mu sarakunan kasar Daura da Katsina babu abinda za mu cewa masu mulki a wannan lokaci, saboda babu irin abun alherin da ba ku yi mana, sai dai mu yi maku fatan alheri. Mun dage da yi maku addu’a, wadda ba sai mun bayyana a fili ba, don samun nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari.
“Duk da ba ni siyasa, amma Ina fatan jam’iyyar APC ta cigaba da mulki a kowane mataki a kasar nan har zuwa shekaru talatin da biyu, kamar yadda na ji ana cewa.”
Mai Martaba Sarkin Daura ya cigaba da cewa, “Ina tabbatar maka dari bisa dari, Ina goyan bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari ko kana bisa kujera da ba ka kai. Duk wanda ke Jihar Katsina da Nijeriya ya san amfaninka da kudurorinka na alheri.”
Sarkin ya kara da cewa, “tabbas ba a taba samu gwamnati, wadda shugabanninta ke kula da talakawa da ririta kudin talakawa da kuma tausaya masu kamar wannan gwamnati ba. Ba mu sani ba ko nan gaba ba! A baya dai babu!
“Don haka muna jinjina maku kuma irin wadannan halaye naku na kirki ku cigaba da su. Ku cigaba da ayyukan alheri da gaskiya da rikon amana da na san ku da shi. Haka sha’anin tsaro, muna yabawa da jinjina ma ka da tausaya maka irin yadda ka ke jajircewa. Kowane mai hankali ya san ana samun sauki, saboda kokarinka ne ba dare ba rana. Allah ya saka da alheri.
Daga karshe, Sarkin ya Jajenta wa ’yan kasuwar da mummunar gobarar ta rutsa da su har suka yi asarar dukiyoyin masu dimbin yawa.
“Ina adduar Allah ya kara tsare gaba. A madadin masarautar Daura da al’ummar Jihar Katsina, Ina mika sakon jajentawa,” a ta bakin Sarkin Daura.
Daga Sagir Abubukar, Katsina