Al’ummar jihar Kano na cigaba da shan azaba a hannun su Ganduje ~Kwankwasiyya

Daya daga marubuta a Gidan Engr Rabi’u Musa kwankwaso Mai suna Abubakar Lecturer ya rubuta inda yake Cewa Watan Ramadan guda ne cikin watannin musulunci da musulmai ke gudanar da ibadar Azumi, wanda ake bukatar duk musulmin kwarai ya himmatu wajen mika wuya ga Allah, da ayyukan neman lada don samun dacewa Duniya da Lahira, tare da taimakon al’umma da dukkan abinda zaka iya.

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shine ya nada kwamishinan ruwa, Sadiq Aminu Wali, ya kuma nada MD na Watar Board, Garba Ahmad Kofar Wambai, dukkan sun gaza a ayyukansu, al’umma sun shiga garari saboda rashin ruwan Famfo, ga Azumi a bakin mutane, ga yanayin zafi da yawaitar hasken Rana, haka zaka riski mutane na fafutukar samun ruwa don amfani, wannan abin kunya ne ga gwamnati, duk ikirarinta na cewa tana samar da ruwa.

Mai girma gwamna, tsananin wahalar ruwa ta ta’azzara a wannan lokacin da musulmi ke ibadah, nasan ana ce maka Khadimul Islam, to wannan abin dai ya isa ya ruguje sunan nan naka a kanka, kayi hobbasa don magance matsalar, hatta mutanen unguwar Gama dake Nasarawa LG, wanda nasan har abada ba zaka manta da unguwar ba, suna cikin wahalar ruwa na tashin hankali, abin kunya shi kwamishinan ruwa dan yankin ne, haka shima MD Water Board, babu ruwa a unguwarsa ta Kofar Wambai.

A bangare guda, kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na jihar Kano (KEDCO), sunyi koyi da gwamnatin jiha wajen gallaza al’ummar Annabi Muhammadu (SAW), tunda watan Ramadan ya kama, shikenan wutar lantarki ta zama sai wane da wane, mu kwanta ba wuta, mu barka da dare babu wuta, mu wayi gari ba wuta, kuma a hakan suke bi suna rarraba takardun bukatar biyansu kudin wuta.

Anan ma dai ina ganin gwamnati tana da rawar takawa wajen ladabtar da kamfanin Kedco, domin bisa zargi suna kai wutar ne zuwa wasu sassa na musamman da suke harkokin kasuwanci, ina kuma kara tuni gareshi shi mai girma Gwamna, yayi kokari don karasa kamma aikin wutar lantarki mallakin jihar Kano, wacce tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso ya fara, ya ajiye kudin aikin a lalitar gwamnati N14.2bn a dam din Tiga da Challawa, domin mutanen Kano su wuta da wannan ukubar daga Kedco.

Zan cigaba…

Abubakar Lecturer
17/04/2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *