Amac Abuja ta Karyata Layla Ali Uthaman Kan rufe gidan abincin ta.

Majalisar karamar hukumar Abuja, AMAC, ta musanta rufe gidan cin abincin wata ‘yar kasuwa mazauniyar Abuja, Layla Ali-Othman.

Kuna iya tuna cewa Ms Ali-Othman a ranar Alhamis din da ta gabata ta nuna bidiyonta a shafinta na sada zumunta, tana mai kuka kan rufe shagon abincin ta ba bisa ka’ida ba daga sashen kudaden shiga na AMAC a yankin Gwarimpa.

Amma mai ba da shawara na musamman ga shugaban AMAC a kan ICT, Abiodun Essiet, ya ce ba jami’an AMAC ne suka aiwatar da hakan ba.

Da take magana da New Agency of Nigeria, Misis Essiet ta ce: “Mun yi bincike a kan lamarin kuma mun gano cewa Sashen Kiwon Lafiyar Jama’a daga FCTA ne ya je gidan cin abincin nata. Ba jami’an AMAC bane.

Ta kara da cewa “Yana da kyau masu kasuwanci su san cewa ba duka kudaden da AMAC ke karba bane,” in ji ta

Don haka, ta shawarci mazauna babban birnin tarayya da su yi taka-tsantsan don kar su afka cikin wadanda suka bayyana a matsayin jami’an kudaden shiga na bogi.

“Ya zama dole ga masu kasuwanci a AMAC su tabbatar da sahihancin mutanen da ke neman su biya wani hakki ko daya.

“Duk wanda zai nuna a matsayin jami’in tattara kudaden shiga dole ne ya samar da katin shaida. Yakamata mutane su dage su dauki hoton jami’in sannan su aiko mana da sako ta hanyar amfani da dandalin sada zumunta

“Nan da nan muka samu irin wadannan sakonnin, za mu amsa.

“Suna kuma iya zuwa sakatariyar karamar hukumar don samun bayani kan batutuwan da suka shafi biyan haraji,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.