Labarai

Amalala: Bola tinubu ya saki fitsari a bainar jama’a ana tsaka da taro.

Spread the love

An hango rigar Bola tinubu da laima wanda ake Zargin fitsari ne yayi a bainar jama’a A Wani faifan bidiyo wanda yanzu haka ya fara yaduwa a kafafen sada zumunta ya nuno jagoran jam’iyyar All Progressives Congress na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu rigarsa a ta jike ta baya a yayin da ya kai ziyara Awujale na Ijebuland.

Tinubu, wanda ke zaune a kan wata bakar doguwar kujera tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar ya tashi domin yin jawabi amma rigar sa ta jike daga baya, musamman a dai-dai wajen kasan duwawunsa.

An ga mai taimaka wa dan siyasar kan harkokin tsaro yana rika rike da hanci a kodayaushe yana duba wurin da aka jika, inda nan take wata mata ta sa abin rufe fuska yayin da Asiwaju ya tashi yana magana.

Hakan dai ya tayar da hankalin ‘yan Najeriya da dama wadanda suka dage cewa Lallai fitsari ne a jikin rigar amma duk da haka wasu sun yi jayayya cewa yana iya zama Kuma gumi ya keto masa sakamakon tsawon lokacin daya kwashe a zaune a kan kujerar ta fata ko Leda.

A halin da ake ciki dai, an samu damuwa game da burin Tinubu a matsayin shugaban kasa duba da kalubalen lafiyarsa.

Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne Tinubu ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Tinubu ya kuma kai ziyara wasu jihohin Arewa da suka hada da Neja da Katsina domin sayar da burinsa.

Ya kuma gana da tsohon shugaban kasar mulkin Soja Janar Ibrahim Babangida, kan shirinsa na zama shugaban kasar Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button