Labarai

Ambaliyar ruwa ta raba mutane 361,000 da muhallansu a jihar Nasarawa

Spread the love

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Nasarawa ta ce akalla mutane 361,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomi takwas cikin 13 na jihar.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Nasarawa, Toto, Doma, Awe, Lafiya, Obi, Karu da Akwanga.

Babban Sakataren Hukumar NASEMA, Zachary Allumaga, ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis a Lafiya cewa akwai yiyuwar ambaliyar ka iya raba mutane miliyan daya da muhallansu a jihar kafin karshen damina.

Allumaga ya ce hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta dauki matakin ne ta hanyar tura tawagar bincike da ceto da jami’anta zuwa kananan hukumomin da al’ummomin da abin ya shafa domin tantance su a nan take.

Ya bayyana cewa jihar Nasarawa na daga cikin jihohin da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta yi hasashen cewa a bana musamman a watan Satumba da Oktoba za a fuskanci mummunar ambaliyar ruwa.

Ya ce, “Hukumar da ke da ikon gwamna ta zagaya ta fara wayar da kan jama’a a yankunan kogin da ke fama da ambaliyar ruwa a kananan hukumomin, Nasarawa, Toto, Doma, Awe, da kuma wuraren da ambaliyar ta mamaye kananan hukumomin, Lafia, Obi, Karu da Akwanga. .

“Mutane kusan 135,000 ne suka rasa matsugunansu a Umaisha, karamar hukumar Toto, 226,000 sun rasa matsugunansu a Nasarawa. An nutsar da al’ummomi biyar a Doma da wasu al’ummomi biyu a karamar hukumar Obi. A yayin da nake magana da ku, mutanenmu suna cikin kogin don tantancewa, bincike da ceto.”

A cewar Allumaga, an yi kokarin taimaka wa ‘yan gudun hijirar da kayayyakin agaji domin rage wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu sakamakon ambaliyar.

Sai dai ya yi kira ga al’ummar da ke zaune a bakin kogi da su tashi zuwa tudu mai tsayi domin gujewa ko wace irin hasara.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne majalisar dokokin jihar Nasarawa ta umurci gwamnatin jihar da ta raba kayan agaji domin rage wahalhalun da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button